An fara garkame layikan salulolin al’umma a Najeriya.
Biyo bayan sanarwar da gwamantin tarayya ta yi, dangane da wadanda basu hada layikan sadarwan su da katin zama dankasa ba.
A jiya gwamnatin tarayya ta fitar da sabon sanarwar duk layin da yau talata 5 Afrilu, ba’a hada shi da lambobin katin ‘Dan kasa ba.
Lallai za su fusakancin fishin Gwamnati a domin kuwa gwamnati ta bada umurnin kukkulle layikan na su.
Rahotanni sun nuna cewar, kamfano nin sadarwar, sun dade suna yiwa masu anfani dasu gargadi.
Kama I zuwa yanzu dai; rahotonni sun bayyana ma wakilin mu cewa! Miliyoyin al’umma ne a Najeriya suka wayi gari a yau talata an garkame layikan salulolin su.
Sakamakon turjiya da suka nunawa Gwamnati na kin hada layikan su da katin zama dan-kasa.”
“Hada layikan salulolin da katin zama Dan kasa yana da nasabar hanyar dakile matsalar tsaro a Najeriya a cewar ita Gwamnatin tarayya”
“Shin ko layin hankar sadarwanka ya gamu da wannan al’amarin kamar yadda wasu mazauna Najeriya suka fuskanta ?.”