Wasu kalamai masu ratsa zuciya da Queen Elizabeth tai kafin rasuwar ta sun bawa kowa mamaki
Rahotanni da su ke fito wa daga Masarautar Buckingham sun nuna cewa Yarima Charles ya zama Sarkin Ingila, bayan rasuwar mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth ta biyu.
Da yammacin Alhamis ɗin nan ne Elizabeth ta mutu tana da shekaru 96 a duniya.
Jaridar AFP ta rawaito cewa, rasuwar ta ta ke da wuya, sai a ka sanar da Charles, wanda shi ke babban ɗanta, mai shekaru 73 da haihuwa, a matsayin wanda zai gaje ta.
Sarauniya Elizabeth dai ita ce mafi daɗewa wa a kan karagar mulkin, inda ta shafe shekaru 70 ta na mulki.
Wasu kalaman da ake tunawa dasu kafin mutuwar Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth.
“Annabi Muhammadu SAW Ya Kasance Mai Nutsuwa Da Tawali’u Wajen Abincin Sa, Kuma Mai Yawan Azumtar Azumi, Bai Shagala A Kan Ɗaukaka Suttura Ba”, Inji Marigayiya Sarauniyar Ingla, Queen Elizabeth II