Uncategory
Anyi Sulhu Tsakanin Fadila Abdulrahman da Hon. Satomi dan majalisar da ake zargin yasa yan daba sun ci zarafin ta a Jihar Borno.
Idan baku manta ba a ‘yan kwanakin nan da suka wuce mun kawo muku labarin wasu ‘yan daba da suka daki wata baiwar Allah mai suna Fadila, wanda sun yi mata hakan ne sabida tayi magana akan wani dan siyasa na jihar Borno mai suna Satomi.
Haka zalika yan daban da aka saka wanan aiki suka fito suna daukar hoto da dollar da aka basu domin aikata wannan danyen aiki.
To shidai Satomi ya nisanta kan sa da aika-aikar da ‘yan dabar suka yi, inda yace bashi da hannu a cin mutuncin da suka yiwa baiwar Allah mai suna Fadila.
Amma daga bisani Dan majalisar yasa an kirawo Fadila Abdulrahm domin zaman yin sulhu da ita inda tace ta hakura da wanan sabani da aka samu da ita.