Bayan kama aminin shahararran dan ta’adda Bello Turji Malam Murtala Sokoto yayi tonon asiri
Bayan kama aminin shahararran dan ta'adda Bello Turji Malam Murtala Sokoto yayi tonon asiri

A cikin wata bidiyo da muka samu daga tashar “Arewarmu Tv” dake kan manhajar Youtube munga Ficaccan Malamin addinin Musulinci Malam Murtala Sokoto yayi tonon asiri, bayan an kama aminin dan ta’adda Bello Turji.
Kamar yadda Malamin yace: Musa Kamarawa bai fadi komai ba a hannun ‘yan sanda, tunda bai fadi mutanen da suke bashi kudi ya sayi dosa cikin tirela guda ya kaiwa su Bello Turji a cikin jeji ba.
Sannan kuma Datti Assalafy ya kara da cewa hakika Gwamnatin Sokoto akwai babban abin zargi a kanta game da wannan ta’addanci dake faruwa a jihar.
Ya kamata masu iko da tsaron tarayyar Nigeria karkashin jagorancin Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari suji wannan sakon sannan a dauki matakin gaggawa da ya dace.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kuji cikekken bayani.