Advertising
Advertising
Labarai

Tashin man Dizel yasa direbobin Tifa sun kara farashin kudin Yashi, Dutse da Kasa

Tashin man Dizel yasa direbobin Tifa sun kara farashin kudin Yashi, Dutse da Kasa

Kungiyar direbobin Tifa ta bayyana cewa, dole sai mun kara farashin yashi, dutse da kasa, ya zama dole ne ta kara farashin yashi, dutse, kasa da sauran kayan gini, sakamakon tashin farashi da kuma wahala ta man dizel.

Advertising

Kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, motocin diban yashi, wanda a hausance a ke kiran su da Tifa da man dizel suke amfani ba
man fetur ba.

Inda tuni man dizel din ya yi tashin gwauron zabi
da ga Naira dari hudu 400 zuwa Naira dari shida da saba’in 670 lita daya, inda kuma ya yi wahalar samu a kasar.

Shugaban Kungiyar Direbobin Tifa reshen jihar Kano “Mamuna Ibrahim Takai” yace babu yadda za’a yi sai an yi karin farashin, in ba haka ba sai dai su tsaya da harkar ta su.

Advertising

A cewar sa, farashin man dizel ya tashi idan
basu kara farashin kayayyakinsu ba, to zasu rika kirga faduwa ne a maimakon riba.

Sannan ya kara da cewa, mataki ne mai wuya amma dole ayi hakuri a karba sabida yanayi ne ya haifar da hakan.

Ya kara da cewa, za’a samu karin farashin yashi da dutse abu ne da ba’a son ran mu ba in ba haka ba sai dai mu rufe kasuwancin namu mu jira lokacin da zai sakko, ayi hakuri yanayi ne ya haifar da hakan.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button