Advertising
Advertising
Labarai

Yadda wasu mata yan uku suka kamu da soyayya Saurayi daya.

Labari mai ban mamaki inda wasu ’yan uku mata ‘yan kasar Kenya suma suka lalubo nasu angon in da suna gab da amarcewa da miji daya. Labarin Eve, Mary da Cate labarine mai ban sha’awa da al’ajabi. ‘Yan uku ne da suka kasance masu kamanni daya hatta da burin su da bukatun su ya kasance ɗaya. ‘Yan uku sun bayyana cewa suna soyayya ne da saurayi daya wanda hakan ya faru ne a lokuta daban-daban.

Advertising

Da yake zantawa da gidan jaridar Amintaciya Matashin, Yace soyayyar su soyayya ce da ke cike da farin ciki domin yana basu kulawa iri daya babu banbanci.

Mary ta labarta cewa Cate ce ta fara haduwa da abin ƙaunar su,kuma batayi kasa a gwiwa ba ta shafa musu labarin, suma kuma nan take su ka bayyana sha’awar su akan shi .
“Cate ce ta fara haduwa da shi tazo ta bamu labari muma kuma nan take Allah ya jarabce mu da son shi” in ji Mary.

Yan matan kara bayyana yadda suka shafe tsawon shekara daya da rabi suna soyayya wanda a yanzu haka suna kan shirye-shiryen aure.

Advertising
Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button