Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wata Mata mai juna biyu tare da wasu mutane 5 matafiya

'Yan bindiga sun yi garkuwa da wata Mata mai juna biyu tare da wasu mutane 5 matafiya

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya shida
wadanda suka hau motar haya ta Jihar Benue, wanda aka fi sani da Benue Links a kan hanyar su ta zuwa Jihar Legas.

Advertising

Kamar yadda Jaridar The Punch ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a ranar Asabar lokacin da motar ta tashi da ga Gboko da fasinjoji 13 amma sai wasu ‘yan bindiga suka tare ta a daidai Ochaja, kusa da Anyingba a Jihar Kogi da
misalin karfe 4 na yamma.

Daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su akwai mace mai juna biyu da wani maraya, inda suka ce direba ya wuce da sauran fasinjojin guda bakwai.

Direban motar mai suna Emmanuel Owoicho ya shaida wa manema labarai cewa, sai da ‘yan bindigar suka yi musu fashi kafin su tafi da fasinjoji shidan.

Advertising

Sannan yace, suna cikin tafiya ne sai ya hango ‘yan bindigar suna fitowa da ga jeji, sai su ka fara harbin iska.

Direban ya kara da cewa, yaso ya tsere amma sai ya tuna cewa zasu bude wa motar wuta shine sai ya tsaya a gefen hanya, inda yace sai ya ga wasu da yawa sun fito da ga jeji suka kuma yi musu fashi.

Ya kara da cewa, sun musu fashin kudade da wayoyi kafin kuma suka yi awon gaba da fasinjoji shidan 6.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button