Advertising
Advertising
Labarai

Bidiyon wata budurwa data chafki yayan marainan wani dan takara shugaban kasa a daidai lokacin da yake kamfen.

Bidiyon Farfesa George Wajackoyah, ‘dan takarar kujerar shugabannin kasa karkashin jamiyyar Roots, yana fuskantar cin zarafi yayin da yake kamfen din darewa kujerar shugabancin kasa.

Advertising

Jaridun kasar sun rahoto yadda lamarin ya faru inda suka ce ‘dan takarar shugaban kasan Kenyan ya fuskanci tururuwar jama’a yayin da yake kamfen din sa a bayan wata akori kura.

Dan takarar shugaban kasan yana tsaka da bayyana jerin abubuwan da zai yi wa kasar ne lokacin da matar ta shigo cikin jama’a tare da yin caraf da mazakutarsa, lamarin da yasa yayi martanin gaggawa.

‘Dan takarar shugaban kasan ya daka tsalle yayin da jami’an tsaron dake biye da shi suka gaggauta daukar mataki, lamarin da yasa matar ta janye hannunta da gaggawa.

Advertising

“Kada ki taba ni” Wajackoyah yace cike da dacin zuciya bayan matar ta yi caraf da yayan nasa.

Dan siyasan ya cigaba da walwalarsa har da wasa da dariya sakanni kadan bayan matar ta janye hannunta daga gabansa.

wannan shine Bidiyon yadda lamarin ya faru.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button