Dalibai zasuyi Azumin Ramadana a gidajen su bayan Gwamnatin Kani ta rage mako data a jadawalin karatun na shekara
Dalibai zasuyi Azumin Ramadana a gidajen su bayan Gwamnatin Kani ta rage mako data a jadawalin karatun na shekara
Gwamnatin Jihar Kano ta baiwa makarantun
gwamnati masu zaman kansu Umarnin rufe makarantu sabida gabatowar Azumin watan Ramadan.
Gwamnatin Kano ta yarda da daidaita jadawalin karatu na makarantun firamare da sakandaren gwamnati da masu zaman kansu a jihar.
Daidaita jadawalin ya biyo bayan koke da iyayen yara suka mika ga gwamnati akan suna rokon gwamnati da’a bada hutu ga yaran domin su sami damar yin azumi a watan Ramadan, duba da muhimmanci watan.
A cewar gwamnatin a sanarwar da Hukumar ilimi ta fitar a yau Talata, za’a rage mako daya a kan mako goma sha uku 13 da yakamata ayi a
zangon karatu na biyu, za’a kara shi zuwa ga
hutun da aka bayar wanda da sati hudu za’a yi
a hutun yanzu ya koma Sati Biyar.
Sabida wannan daidaitawar duk makarantun
gwamnati dama masu zaman kansu dake jihar Kano zasu rufe makarantu da niyyar hutun Sati Biyar daga 1 ga watan Afrilu zuwa 8 ga wata Mayu.
Kwamishinan ilimi Malam Muhammad Sanusi Sa’id ya roki iyaye dasu kula da Yaran su yayin hutun da zai gabato musamman lokacin yanayin tsaro da muke ciki.
Ya kara da cewa, su tabbatar da Yaran suna bitar karatun su da sauraran shirye shiryen ilimi yayin hutu.