Advertising
Advertising
Labarai

Ya kamata Shugaba Buhari ya daure ni da sauran ‘Yan Siyasa sabida mun cuci Nageriya, cewar Tsohon Minista

Ya kamata Shugaba Buhari ya daure ni da sauran 'Yan Siyasa sabida mun cuci Nageriya, cewar Tsohon Minista

Tsohon Ministan Aiyuka Ambasada Ibrahim Musa Kazaure ya bayyana cewa, ya kamata Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kama shi da sauran ‘yan siyasa da suka rike madafun iko ya daure su sabida sun zalunci kasar nan.

Advertising

Da ake zantawa da shi a wani shiri a tashar
Radio France International Kazaure yace, duk yan siyasar Nijeriya daya su ke inda yace babu wani wanda yake yi don talakawa.

A cewar sa, ya fada wa Shugaban Muhammad Buhari da ya kama duk ‘yan siyasar da suka wawashe kudaden gwamnati har da shi.

Tsohon Ministan ya kara da cewa, duk yan siyasan da suka rike madafun iko tun daga 1999 ha su yi wa kasar komai ba, Har ni da nake wannan maganar ya kamata a daure mu sabida ba muyi wa kasar nan komai ba.

Advertising

Na sha fadin cewa, ni Ibrahim Musa Kazaure
mun zalunci Nageriya da talakawan ta magana ta gaskiya ita ce, dukkan mu kanwar ja ce abin da muka yi wa Nijeriya ba haka ya dace mu yi mata ba sabida wasu daga cikin mu sun samu dama wasu kuma basu samu ba.

Ni dai gaskiya na fada, dukkkan mu damu aka yi sata a matse mu mu dawo da kudaden da muka sata, na fada wa Buhari a kame mu a daure mu har sai mun dawo da kudaden da muka sata.

Sannan ya kara da cewa, Ni ba zan sake karbar wani mukami a kasar nan ba ko da kyauta ne.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button