Advertising
Advertising
Labarai

Yadda Malamin Makarantar su yayi masa mummunan duka sabida yaje bara bai kawo masa abinci ba

Yadda Malamin Makarantar su yayi masa mummunan duka sabida yaje bara bai kawo masa abinci ba

A wani labari da muka samu daga shafin wani bawan Allah mai suna “Nasiru Salisu Zango” dake kan dandalin sada zumunta na Facebook, inda ya wallafa wani dogon bayani akan wani yaro da mahaifin sa ya kai shi makarantar Almajiranta jihar Bauchi.

Advertising

Inda malamin makarantar ta yiwa yaran mummunan duka wanda gabadaya ilahirin jikin sa ya kaca-kaca da tabbai, mutumin ya wallafa bayanin cikin wani dogon baya kamar haka.

Labarin da ya motsa min Zuciyam.

Yaro ne karami wanda a fuska ban yi zaton ya haura shekara 8 ba,amma mahaifin sa ya turo shi Kano almajiranci daga garin Gamawa a jihar Bauchi.

Advertising

Ba zuwan sa almajirancin ne yafi damu na ba domin wannan ai an saba,l amma na farko kankantar yaron nan abar dubawa ce, gashi ilahirinjikin sa yayi kaca kaca da tabbai na dukan bulala gaskiya wanda yayi masa wannan dukan ba shi da tausayi kuma bai cancanci ya amsa sunan Malam ba.

Ajawabin da yake baniyaron yace, Malamin sa ne yake dukan sa sabida idan yaje bara baya kawo masa komai, wai ashe idan an fita bara sadakar farko ta Malam ce.

Yaron yaci gaba da cewar, mahaifiyarsa ta rasu kuma mahaifinsa ne ya kawo shi almajiranci kuma yace bai san unguwar da makaramarta su take ba, kwana biyu kenan ya fito bara yayi batan kai ya kasa gane makarantar ta su.

Dan Uwan mai unguwar kofar mata mai suna
Hussaini shine ya karbi yaron daga hannun wadanda suka tsinto shi.

Yanzu haka dai mun hada su da Sani Bundin wani matashi jajircacce dake tsayawa marasa
gata, na kuma hada su da hukumar yaki da bara ta jihar Kano karkashin Sheikh Muhammad AI Bakri mikha’el domin a dauki mataki na Gaba.

Babban abin takaici ne ace har yanzu a Kano ana karbar irin wadannan mini minin yaran da sunan an kawo su bara gaskiya bai dace ba.

Yanzu wannan yaron dai ba’a nuna masa jin kai ba bai samu shakuwa da iyaye ko ‘yan uwa ba, idan ya girma a titi wa kuke tunanin zai tausayawa.

Barin irin wadannan yara da muke gani suna
gararamba a titi babbar masifa ce wacce idan ta
tunkaro bazata takaita akan wanda ya jawo ta ka dai ba, ya kamata mu ribanya kokari wajen yaki da wannan annoba.

Zamanin da dana yanzu ba daya bane ina goyon bayan karatun alkur’ani kuma ina goyon bayan hana bautar da kananan yara.

Allah ya kawo mana karshen matsalolin dake damun Mu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button