Nayi nadamar haihuwar Abubakar Shekau sabida yayi sanadiyar mutuwar al’umma, cewar mahaifiyar sa
A wata doguwar shira da ‘jan jarida sukayi da mahaifiyar shahararran dan ta’adda wanda ya rasu wato Abubakar Shakau, mahaifiyar tasa ta bayyana nadamar ta kan haihuwar sa da tayi sabida yayi sanadiyar mutuwar al’umma da dama a kasar Nageriya.
Jaridar Daily Trust sune suka wallafa bidiyon mahaifiyar Shakau mai suna Falmata Abubakar inda take bayyana al’umma nadamar ta akan haihuwar dan nata Abubakar Shakau, wanda shine shugaban ‘yan ta’adda na Boko Haram.
Shugaban ‘yan Boko Haram Abubakar Shekau ya mutu ne a watan Mayun shekara da 2021 bayan fafata yakin da sukayin da kungiyar ISWAP, wanda yakin ya zamto sanadiyar mutuwar sa tare da dubban mutane.
Kamar yadda masana suka bayyana cewa: Abubakar Shakau yayi sanadiyyar mutuwar al’umma sama da miliyan uku 3 sannan kuma anyi asarar kudaden da suka kai darajar Dalar Amurka Biliyan tara 9.
Abubakar shekau ya kai hare-hare kauyuka da dama wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutanen kauyen sannan kuma suka handame dukiyoyin su.
Babu kauyen da shahararran dan ta’addan wato shekau yake saurarawa kamar kauyen su mai suna shekau idan ka dauke wannan kauyen nasu babu wani kauye ko birni da yake saurarawa.
A cikin bidiyon zakuji yadda mahaifiyar tasa take bayyana cewa, batasan dan nasa wato Abubakar Shekau wanda yana da iyalai, amma tun lokacin da yafara wannan ta’addancin basu kara haduwa ba.
Ga cikekkiyar bidiyon domin ku kalla kuji bayanin da mahaifiyar Abubakar Shekau take.
Application for inpoloment sir please find attached medical certificate for the best for you and your