Bidiyon yadda ake zaro gawar matar da tabi mijinta a mota bayan ta Ganshi da wata budurwa suna tafiya a motar sa.
Wata fitacciyar yar jarida mai suna Marry Nsan, ta yada Bidiyon gawar matar da tabi mijinta a mota bayan ta Ganshi da wata budurwa suna tafiya a motar sa.
Yadda faifan Bidiyon matar da tai mumunan hadarin mota, wadda ake zargin tabi mijinta a motar ne bayan taga shi da wata budurwa sun fito daga wani babban shago.
A labaran baya da muka kawo muku mun labarta muku matar da tabi mijinta bayan ta ganshi da wata mata wanda take zargin kaman suna soyayya ne a garin Calabar jihar kuros Riba.
Yar jarida Merry ta bayyana cewa, marigayiya ta rasu tana da yara, tabi mijin nata ne bayan ta hafu dashi a mota suna fita daga wani babban shagon siyar da kaya. Inda tabishi a motar ta dan shan gaban sa, Sanadiyar da tai mumunan hadari har ta rasa ranta.
Rahotanni sun bayyana cewa mijin nata ya samu nasarar fitar da motar sa ne daga cikin yunkurin da aka yi masa na killace shi, inda ya dauki babbar hanyar Murtala Muhammed, tare da matarsa da zazzafan bin sa.
A kokarin da take yi na ganin ta fi maigidanta, sai ta rasa yadda za ta bi motar da ke gudu, sannan ta kauce hanya sannan ta daki motar a kan bishiya ta kashe kanta.
Yar jarida Merry Nsan ta bayyana haka a shafinta.