Advertising
Advertising
Labarai

An yi kira da a zartar da hukuncin kisa a bainar jama’a kan mutumin daya yiwa Hanifa kisan gilla

Allahu akbar yarinya Hanifa batasan komai ba bata san kaddarar dake jiranta ba haka ma iyayan ta, ashe wanda aka aminta da shi shi ne zai ci amanar ta ya zama silar rayuwar ta.

Advertising

A yanzu dai ita tata ta kare sai dai fatan Allah ya ya bawa iyayan rakurin rashin ta da kuma fatan ganin an dauki mataki mai tsauri akan wadanda suka aikata danyan aikin kisan ta kisan gilla, ba tare da ta musu wani laifi ba balle wacce ko mahaliccin ta taba taba sabawa ba wa zata yiwa laifi.

A jiya dai kunji labarin yadda shugaban makarantar su Hanifa ya bayyana a matsayin wanda ya sace ta kuma ya kashe ta sannan ya shiga hannun hukuma a yayin da yaje karbar kudin fansar ta, da anyi nasara ya karba da haka zai he yaci kudin hankali kwance.

Amma alhaki bai barshi ba tun ba’aje ko’ina ba ya shiga hannu ya fara wulakanta duniya tana masa tofin alatsine kafin yaje rashira ya riski abin da yake jiran sa.

Advertising

Kawo yanzu dai jimamin mutuwar Hanifa da mamakin wannan danyan aiki da malamin nata ya yi bai saki mutane ba, inda ake ta kiraye kiraye ga gwamnati data dauki mataki kan wannan fajirin domin ya zama izina kan masu hali tunani irin nasa, inda Datti Assalafy ya rubuta a shafin sa cewa.

Karshen cin amana kenan hakika zuciya ta kadu matuka da jin labarin mutuwar wannan yarinyar Hanifa a Jihar Kano, da kuma kashe ta da aka yi kisan wulakanci.

Wanda ake zargin ya yi garkuwa da yarinyar malamin makarantar su ne, malamin da ake zargi ya yi mata kisan wulakanci ya binne gawar ta a wajan karbar judin fansa inda aka kama shi yaje ya nuna inda ya binne ta aka tono gawarta aka mata jana’iza.

Malamin da wadan suka taimaka masa sun mata kisan wulakanci sun zuba mata guba a cikin shayi suka bata ta sha, bayan da mutu suka daddatsa gawarta suka je suka binne ta.

Matsalolin garkuwa da mutane yana cigaba da canja salo indai har malami zai iya garkuwa da dalibar sa kamar wannan to dan haka masifa takai masifa, kuma wannan darasi ne ga mu iyaye da muke tura ‘yayan mu makaranta.

Ya kamata a zartarwa da wannan malamin da wadanda suka taya shi hukunci kisa a bainar jama’a, domin ya zama darasi ga masu tunanin aikata laifi irin nasa.

Allah kaji kan Hanifa.

Bayan wannan wallafar da ficaccan marubuci Datti Assalafy ya yi akan mutumin daya aikata wannan yarinyar Hanifa kisan gilla, jama’a da dama sun tofa albarkacin bakun su.

Ku kalli bidiyon dake kasa domin kuji sauran labari.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button