Labarai

Ziyarar Gwamnan kano Abdullahi Ganduje zuwa gidan su Hanifa domin yin ta’aziyya ga iyayan ta

Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyara gidan su marigayiya Hanifa domin ya yiwa iyayan ta ta’aziyya, da kuma basu hakurin rashin da ya same su.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyarar ne tare da masu mara masa baya inda muka ga suna mika ta’aziyyar su ga iyayan, tare da jajanta musu abin da ya faru akan ‘yar tasu.

Bayan zuwan su gidan su Hanifa tare da meka ta’aziyyar su ga iyayan nata sun gudanar da addu’o’i tare da yin wa’azi da nasihohi.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa wanda tashar “Kundin shahara” dake kan manhajar Youtube ta wallafa, domin kuga yadda gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyarar ta’aziyyar sa ga iyayan Hanifa yarinyar da aka mata kisan gilla.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

https://youtu.be/cZ3qI4qAc68

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button