Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan sanda sun yi nasarar kama mutumin da yake taimakawa ‘yan ta’adda yana saya musu motar yaki

Yanzu muka sami labarin wani mutumi da aka kama wanda yake taimakawa ‘yan ta’adda abubuwan da zasu cigaba da al’umma suna kashe mutanen da basuji basu gani ba.

Advertising

Mutumin da bakin sa yake fadin cewa, na taba sayawa dan bindiga kachalla halilu tubali Wanda akafi sani da suna Halilu sububa motar yaki akan kudi N28.5M.

Musa Kamarawa yaran dan ta’adda Bello Turji wanda yake masa safarar makamai yace, akwai lokacin da ya taba sayowa halilu tubali shugaban yanbidigar yammacin Africa motar yaki.

Inda yake bayyana hakan agaban mataimakin shugaban yan”sanda maikula da operation, Zaki Ahmad ranar litinin a lokacin sa aka kama shi.

Advertising

Kamarawa yace akwai lokacin da yaje cotonou jamhuriyar Benin wajen sayen motar yakin amma bai samu ba, sai ya Kira Wani Mai Saida mota a Libya wanda shi dillalin motocin na Libya ne ya bashi lambar wayar Wani mutum a jamhuriyar niger.

Bayan munhadu da wannan mutum na niger shine ya karbi kudi ya kawo mana wannan motar yaki ni kuma na kaiwa kachalla Hali motar, dan uwana Aminu shine yasan hanyar da yabi ya kaiwa kachalla Hali motar yakin a daji.

Ya kara da cewa, mun sayi motar akan kudi naira N28.5 million, amma ina matukar Dana sanin hakan Kuma bazan Kara yin hakaba nakuma yi alkawrin agazawa jami’an tsaro wajen kama duk wani mai tada zaune tsaye inji musa kamarawa.

Mataimakin shugaban ‘yan sanda Zaki ya fadi cewa, tuni ‘yan sanda suka baza komarsu da yin alwashi sai sun karbi motar yakin a duk Inda take.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button