Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan ta’adda sun kone garin Guda tare da yin garkuwa da maigarin da al’ummar sa a lokacin da suka ka hari

Kamar yadda kuka sani har yanzu dai ‘yan ta’adda basu daina kaiwa hare-hare wasu yankuna a Arewacin Nageriya ba, suna hallaka al’umma tare da kwace musu dukiyoyi.

Advertising

Wanda a yanzu haka ‘yan ta’addan suka sake kaiwa wani mummunan hari garin Guda dake karamar hukumar Bakori a jihar Katsina, inda mutanen garin suka wayi gari da mummunan tashin hankali.

Mai magana Datti Assalafiy ya shi ya wallafa laabrin a shafin sa na dandalin sada zumunta Facebook, inda ya wallafa labarin kamar haka.

DON ALLAH GWAMNATI KU DAUKI MATAKI.

Advertising

Jiya Litinin da misalin karfe 10:00pm na dare
annoba ‘yan ta’addan jeji sun yiwa al’ummar garin Guga dake karamar hukumar Bakori Jihar Katsina kawanya, mutanen garin sun wayi garin yau da wani mummunan harin ‘yan ta’adda da ya rutsa da su.

Harin ya hallaka rayukan bayin Allah wadanda basu ji basu gani ba talakawa gajiyayyu marassa karfi, ‘yan ta’adda sun kashe rayukan maza da mata manya da kananan yara a garin Guga.

Bayan haka, ‘yan ta’addan sun wawushe makudan kudaden al’ummar garin tare da kone dukiyoyin jama’a da manyan shaguna da kuma kayan abinci.

Sannan maharan sun tafi da dunbin mutane wanda kawo yanzu ba’a san adadinsu ba, kuma cikin mutanen da aka tafi da su har da maigarin Guga yana cikin wadanda ‘yan ta’addan sukayi garkuwa da su.

Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya wannan shine abinda ya faru daren jiya a jihar ka ta asali kuma a Gwamnatin ka.

Ana kafa Gwamnati domin ta kawo doka da
oda ta tsare rayuka da dukiyoyin al’ummah
idan aka rasa wannan to babu amfanin.

Bai kamata masu iko su tare da matan su da iyalan su a babban birnin tarayya Abuja jami’an tsaro sun gadinsu sannan a bar talakawa a hannun ‘yan ta’adda ba.

Don haka muna jawo hankalin masu iko da
Gwamnati su ji tsoron Allah su dauki mummunan mataki akan ‘yan ta’adda, ku sani
Allah ba azzalumin bawan sa bane Allah yana da hanyoyi masu yawa da zai kama ku mummunan damka da kamu.

Ga hotunan yadda ‘yan ta’addan suka yiwa garin fata-fata suka saka masa wuta tare da kone dukiyoyin al’ummar garin.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button