Advertising
Advertising
Labarai

Zamu iya mika Abba Kyari ga Amurka kan tuhume-tuhumen da ake masa idan suka bukaci haka, inji Abubakar Malami

Zamu iya mika Abba Kyari ga kasar Amurka kan tuhume-tuhumen da ake masa idan suka bukaci haka, inji Abubakar Malami

‘Yan sandan Najeriya sun fara bincike akan tuhume-tuhumen da ake wa “DCP Abba kyari” ne bayan da wasu bayanai suka fito daga hukumar ‘yan sanda ta FBI kan alakar sa da dan damfara Hushpuppi wanda a halin yanzu ke tsare a wani kurkukun Amurka.

Advertising

Hukumomin Najeriya zasu iya mika wa kasar Amurka jami’in dan sanda “DCP Abba kyari” domin ya fuskanci dukkannin tuhume-tuhumen da hukumar ‘yan sandan kasar Amurka ta FBI ke yi masa idan bukatar haka ta taso.

Ministan shari’a na kasar Najeriya mai suna “Abubakar Malami” shi ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da yayi da tashar talabijin ta Channels.

Inda Minista Abubakar Malami yake cewa, hukumomin Najeriya suna aiki tare da jami’an Amurka akan tuhume-tuhumen da ake yiwa “DCP Abba Kyari” da mutumin da ake tuhuma da aikata damfara ta intanet wato Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Advertising

Wannan batu ne da ya shafi yin aiki tare tsakanin kasa da kasa kuma muna aiki tare, kana ana samun cigaba.

Sai dai Minista Abubakar Malami bai ce komai ba kan abin da gwamnatin kasar Najeriya zata yi, idan Amurka ta bukaci a mika mata “DCP Abba Kyari” in ban da cewa kawo yanzu kasashe na cigaba da duba batun.

Akwai batutuwa masu yawa da muke dubawa ciki har da yiwuwar mika “DCP Abba Kyari”, sabida haka ne hadin kai kan batun ke da muhimmanci matuka kan wadannan batutuwan.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button