Advertising
Advertising
Labarai

Alakar dake tsakanin Shugaban Kasa Buhari da ‘yan Nageriya tamkar auren dole ne, inji Aminu Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammad Buhari bai fahimci ta yadda ake tafiyar da shugabancin zamani ba.

Advertising

A ranar 19 ga watan Maris ne Tambuwal ya bayyana cewa, alakar dake tsakanin shugaba Muhammad Buhari da ‘yan kasar Nagwriya kamar auren dole ne.

Da yake magana a sakatariyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kaduna, gwamnan na jihar Sokoto ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC da lalata kasar.

Tambuwal yake cewa: Mun ga cewa APC ba ta iya ba kuma ba za ta iya kula da harkokinsu a matsayin jam’iyya ba. Ta yaya za ta iya samar da mulki da shugabancin kasa mai girma da wuyan sha’ani kamar Najeriya? Mun san rikicin APC a yau.

Advertising

Na fadi wannan a wani wajan kuma zan maimaita, lamarin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Najeriya tamkar auren dole ne tsakanin namiji da mace.

Da wuya a samu fahimta ko zaman lafiya. Shugaban kasar bai fahimci Najeriya da yadda ake tafiyar da shugabancin zamani ba.

Tambuwal ya kara da cewa: Najeriya na bukatar shugaba wanda ya fahimci kasar kuma wanda zai iya samar da daidaito kan muhimman al’amuran da suka shafi kasa.

Domin ganin mun magance matsalolin Najeriya a yau, akwai bukatar mu samu babban jagoran kasar nan mutumin da ya fahimci Najeriya da kanta. Wadanda ke da abokai a duk wani lungu da sako na kasar nan.

Za su iya tuntuba sannan su dauki hukuncin bai daya kan lamuran da suka shafi mutanen kasar nan. Za ka iya aikata hakan ne kawai idan kana da hanyar sadarwar da ake bukata.

Muna bukatar mutum da zai iya hada kan kasar nan. Mutum da ya ke tsantsar dan Najeriya. Wanda ya fahimci yanayin shugabanci na zamani.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button