Tirkashi: Matashin Daya ce Buhari zai hadarin jirgi a tafiyar sa ya fito ya janye kalaman sa.
Wani bawan Allah mai suna Ahmed Abubakar Sadiq ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari fatan yin hadarin jirgin sama a hanyar sa ta dawo daga kasar Belgium a taron kasashen AU.
Matashin mai suna Ahamd Abubakar Sadiq Ya wallafa sakon a shafin sa daga bisani kuma ya goge shi bayan ganin an fara yada maganar tasa.
Sai dai wani mutun yayi masa magana ta sashin tsokaci yake cewa
Zai yi kyau idan @Police NG ta gayyaci @audisadiq2 don Ζ™arin bayani game da wannan tweet. Watakila yana cikin ‘yan ta’adda a Najeriya da ya fi sanin wasu bayanai da suka dace da sakonsa na twitter.
Tuni matashin ya maidawa mutumin da yayi tsokaci marrani akan cewar bashi ya wallafa sakon ba.. Masu kutse ne sukai hasalima shi babba masoyin Shugaba Muhammad Buhari ne baya wallafa irin wannan abu buwan.