Labarai

Shugaba Buhari ya yabawa Bankin Masana’antau bisa samar da ayyukan yi sama da Miliyan tara

Shugaba Buhari ya yabawa Bankin Masana'antau bisa samar da ayyukan yi sama da Miliyan tara

A wani labari da muka sami daga shafin Daily Nigerian Hausa, sun wallafa cewa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba
wa Bankin Masana’antu “BOI” bisa samar da ayyukan yi sama da miliyan tara a cikin shekaru bakwai da su ka gabata.

Ya kuma yaba wa “BOI” bisa yadda ya raba sama da Naira Tiriliyan 1.24 ga ma’aikata miliyan 4.2 da suka amfana a kanana matsakaita da manyan masana’antu.

Shugaban ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya kaddamar da dogon gini na biyu na “BOI” a Abuja a ranar Alhamis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button