Cigaba ya wado Masana’antar Kannywood bayan rikicin da akai fama dashi a ciki.
Cigaba ya wado cikin Masana’antar Kannywood bayan rikicin da akai fama dashi a ciki.
Alamu sun nuna cewa rigimar da ake fama da ita akan Ladin cima ta samu ruwan sani, Tabbas hausawa na cewa ba’a taba samun cigaba cikin sauki matukar ba’a kai ruwa rana ba.
A halin yanzu Masana’antar ta samu wani cigaba da ake ta son samunsa sa wanda aka gaza samu tun a baya wanda ake ganin cewar shine yaja rikicin da akai ta fama dashi a masana’antar ta kannywood. Har ta kai mutanen gari nayiwa jaruman dariya wasu ma na kallon cewar dama macuta ne a harkar.
To yanzu dai a takaice an kafa kwamiti mai karfi a cikin masana’antar Kannywood, wanda zai dinga aiki wajen taimakawa tsoffin jarumai da marasa karfi da kuma marayu, wadanda iyayen su suka rasu a cikin masana’antar.
Tambarin Hausa sun hada mana rahoto akan wannan labari.