Advertising
Advertising
Labarai

Sojojin kasar Rasha sun zagaye birnin Sumy inda Daliban Nageriya ke makale a ciki a Ukraniya

Kamar yadda aka bayyana cewa, kimanin ‘yan Nageriya dari uku da saba’in ne suka tsare a wani birnin Ukraniya, wanda sojojin Rasha suka zagaye.

Advertising

Daliban da suka makale din suna cikin barazana da cutarwa sakamakon sojojin kasar Rasha sun kara maida hankali wajan kai hare-hare a biranen kasar ta Ukraniya, a yakin da ya shiga raba ta bakwai 7 wato ranar Laraba.

Sakatare na biyu 2 a ofishin jakadancin Ukraniya a Nageriya babban birnin tarayya Abuja “Bohdan Soltys” shi ne ya bayyana hakan, a lokacin shira da jaridar Leadership a ranar Laraba.

Inda yaje cewa, Daliban Najeriya dake cikin birnin Sumy sun makale sannan kuma babu wata hanyar fita daga birnin sabida sojojin Rasha sun zagaye shi baki daya.

Advertising

Inda ya roki gwamnatin tarayya da kungiyoyin kasa da kasa, musamman hukumomin jin kai su gaggauta yin wani abu domin tseratar da Daliban Najeriya daga mamayar sojojin Rasha.

Daga Comr Abba Sani Pantami.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button