Yadda mayakan Boko haramun suka yiwa mutun 11 yankan rago.
Wasu Maharan sun ajiye baburansu ne sannan suka shiga garin a kafa suka yi aika-aikar a ranar Laraba, a garin Geidam, mahaifar Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali-Baba.
Wasu rahotanni na cewa adadin mutanen da kungiyar ta ISWAP ta yi wa yankan rago sun kai 11, sai dai kawo yanzu hukumomi ba su yi magana kan lamarin ba.
Jaridar Aminiya ta gano cewa ’yan ta’addar sun yi yunkurin shiga garin na Geidam ne tun kusan magariba, a ranar Laraba amma sojoji da ke garin suka fatattake su.
Daga baya cikin dare wajen karfe 11 suka sulalo zuwa cikin garin ta unguwar Marawa a kusa da Makarantar Sakandaren Kimiyya, inda yanka mutum guda.
Daga nan suka wuce zuwa Unguwar Kwari suka yanka wasu mutum takwas ciki har da wata mace.
Wani magidanci a Unguwar Kwari ya shaida wa Aminiya ta waya cewa ’yan ta’addar sun shiga garin ne da misalin karfe 11.00 na dare, suka nufi wani wata mashaya a unguwar, inda suka yi wa mutum takwas yankan rago tare da raunata wasu biyu.
Mazauna yankin sun kara bayyana cewa maharan sun shammace su da kuma sojojin da ke Geidam ba saboda ba a yi artabu ba.
A cewarsu, sun yi aiwatar da wannan aika-aika ne cikin sirri sannan suka fice suka tsere.
Ko da yake sojoji da samun labarin sun mayar da martani cikin gaggawa suka bi sawunsu, amma majiyarmu ta ce maharan tuni suka tsere zuwa cikin daji ba tare da sojojin sun cin musu ba.
Har zuwa lokacin kammala wannan wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su tabbatar da harin ko cewa wani abu kan wannan hari ba sai dai nan gaba.