Advertising
Advertising
Labarai

Sojojin Nageriya sun hallaka ‘yan ta’adda a kalla 200 a wani harin sumame da suka kai musu

Sojojin Nageriya sun hallaka 'yan ta'adda a kalla 200 a wani harin sumame da suka kai musu

Har yanzu dai Sojojin Nageriya suna yin nasara kan yakar ‘yan ta’addan da suke hallaka al’ummar da basu ji basu gani ba, musamman a Arewacin kasar Nageriya.

Advertising

Wanda a yanzu haka muka sami kyakkyawan labari game da nasarar da Sojojin Nageriya suka samu akan ‘yan ta’addan, kamar yadda shafin Daily Nigerian Hausa suka wallafa labarin kamar haka.

Rundunar Sojin Nijeriya ta hallaka a kalla ‘yan
ta’adda guda dari biyu 200 a wani sumame da sojojin suka kai kan maboyar yan ta’addan a kauyen Ghana da ke Karamar Hukumar Mariga a
Jihar Naija.

PR Nigeria ta ruwaito cewa, ‘yan ta’addan sun
gamu da ajalin su ne a jiya Laraba bayan da
jiragen yakin sojoji, karkashin rundunar sojin
Operation Thunder Strike da kuma Operation
Gama Aiki suka yi musu luguden wuta ta sama.

Advertising

Kamar yadda Rahoton ya bayyana cewa, an kai wa yan ta’addan sumamen ne da misalin karfe 4:45 da kuma karfe 6:34, a wasu sansanonin su dake Ghana.

Kamar dai yadda PR Nigeria ta ruwaito cewa, an dade ana fakon ‘yan ta’addan inda aka gano cewa sun kasa kan su zuwa rukuni-rukuni na mutum arba’in 40 kuma da baburan ashirin da biyar-biyar.

A maimakon dakarun su yaki rukuni-rukuni
daban-daban na ‘yan ta’addan wanda hakan ba lallai a sami abinda ake so ba, sai suka hakura suka cigaba da fakon su har sai da suka hadu a waje guda a yankin Ghana, inda sojojin suka afka musu suka hallaka dari biyu 200 daga cikin su.

Wata majiyar sirri da ga bangaren sojoji ta bayyana cewa, a kalla ‘yan ta’adda dari da hamsin 150 sun hallaka nan take a harin, inda Majiyar ta kara cewa wadanda suka tsere da
raunuka a jikin su, sai sojojin kasa kuma suka afka musu suka gama da su.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button