An tasa keyar mai wasan barkwanci da na’ibin sa zuwa gidan maza sakamakon bata sunan gwamnatin Jihar kano.
A safiyar yau Laraba Kotun Majistiri mai lamba 58 da ke Nomansland a Kano ta aike da wasu matasa masu wasan barkwanci zuwa gidan garan hali bisa wani laiafi da sukai wa gwamnatin Jihar.
An gurfanar da matasan yan wasan Barkwancin Mubarak Muhammad da aka fi sani da Uniquepikin da mai ja masa baki Nazifi Isah Muhammad a gaban Kotun bisa zarge-zarge guda hudu da ake musu.
Hukumar tace fina-finai ta Kano karkashin jagorancin Ismail na Abba Afakallah ce tayi kararsu bisa zargin hada kai da cin zarafin gwamanti jihar kano da bata mata suna bata suna, Dr. Abdullahi Umar Ganduje tare da yunkurin tayar da hayaniya a wani faifan bidiyo da suka fitar a shafin su.
Yayin zaman Kotun na yau Laraba wadanda ake zargin sun amsa tuhumar da ake musu.
Lauyan da ke kare su da iyayensu, sun roki kotu da ta yi musu afuwa.
A nan ne kuma alkalin Kotun mai shari’a Aminu Gabari ya dage shari’ar zuwa ranar Litinin 7 ga watan Nuwamban da muke ciki.