Advertising
Advertising
Labarai

Aliko Dangote ya bayar da babbar gudunmawar inganta tsaro a kasar Nageriya, inji Ministan tsaro Magashi

Aliko Dangote ya bayar da babbar gudunmawar inganta tsaro a kasar Nageriya, inji Ministan tsaro Magashi

Ministan Tsaro mai suna Bashir Salihi Magashi ya bayyana cewa, Kamfanin Dangote ya bada gudunmawa gagarumar wajen inganta tsaro a Nijeriya, bayan la’akari da yadda yake zuba jari mai yawa da kuma samar da ayyukan yi a kasar.

Advertising

Magashi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a lokacin da ya ziyarci rumfar Dangote a wajen bikin baje kolin kasa da kasa, karo na 43 a jihar Kaduna.

Ministan wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa “Manjo Janar Ahmed Tijani Jibrin” (Rtd) yace, kamfanin ya yi tasiri sosai wajen inganta tsaro ta hanyar samar da ayyukan yi a kasar nan, kamar yadda sanarwar da ga sashin yada labarai na kamfanin ta bayyana.

Daily Nigerian Hausa ta gano cewa, bayan gwamnatin tarayya Dangote ne na biyu wajen samar da aikin yi a Nigeria, Dangote ne babban wanda ke daukar nauyin baje kolin kasuwanci na Kaduna da ake yi.

Advertising

A cewar Magashi, bincike ya nuna akwai alaka tsakanin yanayin tattalin arziki da tsaro inda yace rukunin Kamfanonin Dangote ba wai samar da ayyukan yi kadai yake yi ba, har da tallafawa wajen samar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.

Sanarwar tace, mahalarta taron dake neman yin kasuwanci da duk wani reshen kamfanin na iya cin gajiyar irin wannan damar a rumfar Kamfanin.

Ta bayyana jihar Kaduna a matsayin daya daga cikin manyan kasuwanninta a kasar nan, idan aka yi la’akari da matsayinta na tarihi a matsayin hedkwatar siyasar Arewacin Najeriya.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button