Labarai

Shugaba Muhammad Buhari ya sanya hannu a akan sabuwar Dokar Zabe a Kasar Nageriya

Shugaba Muhammad Buhari ya sanya hannu a akan sabuwar Dokar Zabe a Kasar Nageriya

Shugaban kasar Nageriya Muhammad Buhari ya sanya hannu akan sabuwar dokar Zabe domin samar da wasu sabbin gyare-gyare a harkar Zabe ta kasar Nageriya.

Shugaba Muhammad Byhari ya sanya hannun ne a lokacij da aka gudanar da wani shagalin biki a fadar sa, wanda a lokacin shugaban Majalistar Dattawa Sen, Ahmad Lawal da Shugaban Majalistar Wakilai da Femi Gbajabeimila suna wajan.

A gyare-gyaren da aka yiwa dokar Zaben kowanne mai rike da mukamin siyasa ko ma’aikacin gwamnati, zai ajiye mukamin sa a watanni shida 6 idan har zai iya takara.

A jawabin shugaba Muhammad Buhari ya bukaci ‘yan majalista su hanzarta yin gyara ga sashe na tamanun da hudu 84 na dokar, wanda ya tanadi haramtawa masu rike da mukaman gwamnati jefa kuri’a a zaben shugabannin jam’iyya ko kuma na ‘yan takara.

Rahoto Daga Comr Nura Siniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button