Advertising
Advertising
Labarai

Allah Sarki: Wasu Malamai Mata Uku Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kaduna.

Wasu Malamai Mata Uku Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kaduna.

Advertising

An jefa daukacin ma’aikatan makarantar Shehu Idris College Of Health Science & Technology (SIIHST) Makarfi da ke jihar Kaduna cikin alhini sakamakon rasuwar wasu malamai mata uku.

AInside Arewa Media, Ta rawaito Malaman sun mutu ne a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a Gwargwaji, a Zariya a yammacin ranar Litinin, 30 ga watan Mayu, a hanyar su ta dawowa daga aiki.

Wadanda suka rasun an bayyana sunayensu da Mrs Adanna Joan Nwafor, babbar jami’a a Sashen Kimiyar Kiwon Lafiyar Al’umma, Mrs Amina Tahir, Ma’aikatar Kimiyar Kiwon Lafiyar Al’umma da Madam Rabi’atu Malami Dogo, babbar jami’a a sashen kula da hakora.

Advertising

Malama ta hudu mai suna Misis Kafayat Abdulrashed ta Sashen MIT ta tsira kuma a halin yanzu tana jinya a asibiti.

Mana fatan allaha ya kiyaye gaba Amin.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button