Advertising
Advertising
Labarai

Gargadin Shugaba Buhari kan masu nunawa juna yatsa akan rikicin jam’iyyar APC

Gargadin Shugaba Buhari kan masu nunawa juna yatsa akan rikicin jam'iyyar APC

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi
gargadi ga shugabanni da yan jam’iyar APC
da su dena nuna wa juna yatsa da sa’in sa a
junan su, ya yin da jam’iyar ke tunkarar babban
taron ta na kasa a ranar ashirin da shida 26 ga watan Maris.

Advertising

Kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, APC ta sake nutsa wa cikin rikici bayan da
gwamnoni goma sha tara 19 karkashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufai, suka ham barar da kujerar Shugaban kwamitin riko na jam’iyar “Gwamna Mai Mala Buni” inda ake zargin da umarnin Shugaban kasa suka aikata hakan.

Daga bisani sai shugaba Buhari ya ja kunnen ‘yan jam’iyar da su cigaba da jajircewa da hada
kai domin jam’iyar ta cigaba da tafiya akan
gwadabenta na nasara data ke kai.

Sannan kuma shugaba Buhari ya kuma buga misali da jam’iyar adawa ta PDP inda yace, duk karfin ta a kasar nan amma yanzu ta yi kasa.

Advertising

A sanarwar da kakakin sa Garba Shehu ya
fitar shugaba Buhari yace, APC ta kwashe kusan
shekaru takwas 8 tana mamaye sauran jam’iyyu
sabida ta bude kofar ta ga duk wanda yanke so ya shigo daga wata jam’iya babba ko karama.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button