Matashin da yake tsarewa ‘yam mata yana neman lalata musu rayuwa ya gamu da fishin Datti Assalafy
Matashin da yake tsarewa 'yam mata yana neman lalata musu rayuwa ya gamu da fishin Datti Assalafy
Shahararran marubucin nan Datti Assalafy ya wallafa wata bidiyo tare da wani rubutu a shafin sa na sada zumunta istagram kan wani matashi.
Wanda yake tsarewa mata ‘yan makarantar Ado Bayero yana musu tambayoyi idan sun amsa sai ya kyale su idan kuma basu amsa ba sai yace zai mare su ko kuma su masa kiss wato sumbata.
Datti Assalafy ya wallafa rubutun nasa akan matashin kamar haka.
Ga wani matashi Musulmi Bahaushe mai kitso a
kanshi da gashi, yana yawan zuwa Ado Bayero Mall Kano yana tare ‘yan matan mutane da suka je sayayya yana yin hira da su, sannan yaje ya daura a shafinsa na Tiktok.
Kamar yadda zaku gani a wannan bidiyon, abinda matashin yake yi kenan, sai ya sa budurwa ta zabi ya mata kiss ko mari bayan ya gama hira da su, kamar yadda yasa wannan yarinya ta masa kiss, daga nan sai yaje ya daura a shafinsa na Tiktok.
Wannan dabi’ar a kasashen Yahudawa ake yinta, yau mun wayi gari ga wani ‘dan Musulmai ya kawo dabi’ar garin Kano.
Muna kira ga rundinar Musulunci Hisbah reshenjihar Kano ta gaggauta daukar matakin da ya dace domin bai fl karfin doka ba.
Muna rokon Allah Ya karemu daga sharrin fitinar
karshen zamani.
Bayan wannan wallafar rubutun da ya yi sai kuma ya sake wallafa bidiyon matashin, kamar yadda zakuga bidiyon a kasa.