Labarai
Hukumar hisbah ta bude shafi a TikTok saboda kawo gyara a harkar.
HISBAH ta bude shafi a dandalin @TikTok
Hukumar HISBAH ta jihar Kano karkashin jagoranci Ibnisina ta bude shafinta a dandalin Tik Tok inda take wallafa bayanan ayyukanta da nasihohi a cikin bidiyo.
Dandalin Tik Tok dai ya zama wata kafar sada zumunta da ake yawan samun wasu bata gari da suke haddasa masifu da dama a kanta.
Ana tunanin wannan dalilin ne yasa hukumar taga ya dace su bude shafin su suma a manhajar.
Muna so muji Ra’ayoyin ku a kan wannan lamarin.