Labarai

Kungiyar Miyatti Allah ta nuna bacin ranta kan zargin kashewa ‘yayan ta shanu da ake a jihar Filato

Kungiyar fulani ta miyatti Allah tayi zargin cewa, ga dukkan alamu an bullo da wani sabon salo na kashewa shanun ‘yayan su a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Shugaban kungiyar na miyatti Allah mai suna Ya’u Idris ya yi wannan zargin ne a cikin wata shira da manema labarai suka yi da shi da yammacin ranar Litinin.

Inda a cikin shirar yake bayyana cewa, makiyaya sun rasa shanun su sama sa ashirin 20 a cikin wannan watan na Maris inda har yayi zargin cewa.

Ana sanya guba ne a cikin ruwan da shanun suke sha da kuma ‘yayan mangwaron da ake zubarwa a kasa shanun suna sha.

Ya’u Idris ya fadi cewa, a binciken da likitocin dabbobi suka yi ya nuna cewa guba ce ta hallaka shanun da aka yi gwajin gano musabbabin mutuwar su.

Sannan ya yi kira da Gwamnati da hukumomi domin su dauki matakin da ya dace da nufin hana sake tashin rikici tsakanin makiyaya da manoma a yankin da kuma jihar baki daya.

Jaridar RTV ta ruwaito cewa, a yanzu dai ba’a ji ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato ba dangane da lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button