Advertising
Advertising
Labarai

Shugaba Muhammad Buhari ya yi Allah wadai da harin Bam din da ‘yan ta’adda suka kai jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

Kamar yadda labari da hotuna suka yi ta yawo a kafafun sada zumunta kan cewa, wasu ‘yan ta’adda sun saka Bam a hanyar jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna inda wasu daga ciki suka rasa rayukan su wasu kuma suka raunata.

Advertising

Inda bayan faruwan hakan ‘yan ta’addan suka kara budewa jirgin wuta har ma suka shiga cikin sa suka fashi, lamarin da ya yi matukar tadawa al’umma hankali.

To a yanzu kuma mun sami labarin cewa, Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya yi Allah wadai da harin bam da aka kai wa jirgin kasa da ke dauke da fasinja kusan 1000, a hanyar Abuja zuwa Kaduna yana mai bayyana al’amarin a matsayin wani abin damuwa matuka.

A cikin sanarwar da fadar shugaban ta fitar Shugaba Buhari ya bayyana cewa, kamar sauran ‘yan Najeriya ina cikin jimami matuka da faruwar wannan lamarin, wanda shi ne irinsa na biyu wanda ya kai ga sanadin mutuwar fasinjojin da har yanzu ba’a tantance adadinsu ba da kuma wasu da suka samu raunuka.

Advertising

Shugaba Buhari yace, Harin da aka kai kan jirgin kasa abin takaici ne tunani na yana kan iyalan wadanda suka rasu da kuma addu’a ga wadanda suka jikkata.

Inda ya kara da cewa, ya bayar da umarnin gaggawa na tabbatar da bincike da hanyoyin magance matsalar tsaron titin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna.

Sannan ya umarci jami’an tsaro su kubutar da fasinjojin da daka sace tare da farautar ‘yn ta’addan, bayanai sun nuna cewa kimanin mutum 1000 ne a cikin jirgin wanda aka kai wa hari ranar Litinin da daddare.

Rahotanni sun ce, an sace mutane da dama sannan an kashe wasu, abin da ya jijjiga iyalai da ‘yan uwan fasinjojin dake cikin jirgin.

Daga Comr Abba Sani Pantami

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button