Advertising
Advertising
Labarai

Attajiri Ned Nwoko ya yiwa Jaruma Empire zazzafan martani kan cewa ita ta hadawa Amaryar sa maganin Ni’ima da har ya kori uwar gidan sa

Shahararran dan kasuwar nan mai suna “Ned Nwoko” wanda yake kudancin Kasar Nageriya yayi zazzafan martani akan wani labarin da Ficacciyar mai sai da kayan mata Hauwa Sa’idu wacce aka sanin ta da Jaruma.

Advertising

Inda ta bayyana cewa: sabida kayan matan data baiwa amaryar sa ne yayi sanadiyyar rabuwar da daya matar tasa wato uwar gidan sa, mai suna Laila Charani Kasar Marocco.

Sai dai Ned Nwoko bai kyale wannan magar da Jaruma ta fada masa inda ya mai da mata da martani da cewa, idan har kayan matan da take sai dawa mai yasa ta kasa ruke Mijin ta da shi, har ta bari auren su ya mutu.

Kamar yadda wata majiya mai suna “Muryoyi” ta ruwaito irin rikicin da ya kaure tsakanin Ned Nwoko da uwar gidan nasa Laila Charani ‘yar kasar Marocco, bayan da ya aure wata jarumar Fim mai suna Regina Daiels wanda har ta kai ga ya saki uwar gidan nasa.

Advertising

Bayan faruwar wannan al’amarin ne yasa Jaruma mai kayan Mata take fadin cewa, kayan Matan da ta bawa Amaryar Ned Nwoko mai suna Regina Daiels ne ya rude shi har ya saki uwar gidan nasa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button