Wata matar aure ta aike da mijinta har lahira sanadiyar zai kara Aure.
Wani rahoto dake fita ranar Litinin 4 ga wata April, wata matar Aure Wadda take dauke da juna biyu mai suna Omowunmi yar unguwar Odeye a yankin Alaadarin dake karamar hukumar ibadan jihar Arewa oyo, Ta cakawa mijinta joseph Nwanko wuka mai da misalib karfe biyu na dare lokacin da yake bacci.
Tun da farko jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rigima ta barke a tsakanin ma’auratan sati biyu da su ka wuce bayan da mijin ya shaidawa matar cewa yana son yi mata kishiya daga ƙauyen sa.
An samo cewa bayan ta aikata laifin, Omowunmi ta miƙa kan ta zuwa ofishin ‘yan sanda na Iyaganku inda daga nan aka wuce da ita zuwa ofishin hukumar na Yemetu, wanda ya ke kusa da inda lamarin ya auku.
Jaridar ta Daily Trust ta ziyarci ofishin ‘yan sandan na Yemetu da safiyar ranar Litinin 4 ga watan Afrilu, inda ta samu cewa an miƙa gawar mamacin zuwa mutuware.
Har ya zuwa yanzu, baa ji ta bakin kakakin hukumar ‘yan sandan jihar ta Oyo, Adewale Osifefo, ba dangane da lamarin.