Jami’an Sojoji su kama wani dan leken asirin ‘yan Boko Haram/ISWAP da ake neman sa ruwa a jallo a jihar Borno
Jami'an Sojoji su kama wani dan leken asirin 'yan Boko Haram/ISWAP da ake neman sa ruwa a jallo a jihar Borno
A wani labari da muka samu daga shafin “Hausaloaded” mun ji cewa, Rundunar sojojin Najeriya ta 21 Special Forces Brigade, dake Bama, sun kama wani babban jami’in leken asiri na kungiyar Boko Haram/ISWAP da ake nema ruwa a jallo mai suna “Modu Babagana”, wanda ya tsere daga tsare daga magarkamar sojoji a garin Bama.
An taba kama dan leken asirin Babagana a watan Janairun 2020 bayan an sake shi yqna gudanar da ayyukan leken asiri kan sojoji a yankin Bama da Banki.
Kwanaki kadan bayan da aka kai shi gidan yari, ya yi amfani da asiri wajen fasa gidan yari tare da kaucewa kamun jami’an tsaro har ya tsere.
Bayan sojojin dake tsare da gidan yarin suka ya tsere sai suka bayyana cewa, ana nemansa tare da yada hotunansa a kowane lungu da sako na birnin.
Sa’ar ta kure masa, a lokacin da aka sake kama shi tare da taimakon jiga-jigan rundunar hadin gwiwa ta Civilian Task Force a babbar kasuwar Bama, a lokacin da yaje aiken sayo kayan aiki ga ‘yan ta’adda da makudan kudade.
A yayin gudanar da bincike na farko dan leken asirin ya amsa cewa, shine yake sa ido tare da bayyanawa ‘yan ta’addan inda sojojin suke da kuma dukkan motsin su.