Advertising
Advertising
Labarai

Yadda wani matashi ya rasa Ransa a gidan kallon ball yayin wasan Real Madrid.

A ranar Laraba da dare an yi wasan kwallo tsakanin kungiyoyi biyu, Real Madrid da Man City wanda ya yi matukar daukar hankalin matasa musamamn masu son wasannin kwallo.

Advertising

Wasan wanda ya kai har karfe 11 saura na dare ya tashi ne yayin da wasu su ke kunci, wasu kuma su ka dinga farin ciki don Real Madrid ta ci Man City.

Sai dai babu wanda zai iya bayyana musababbin mutuwar matashin don babu wanda ya lura da cewa ya rasu har sai da kowa ya watse ana tunanin bacci ne ya dauke shi.

Wani matashi wanda ya bukaci a sakaya sunansa, wanda shi ma ya yi kallon kwallo a gidan ya bayyana wa LabarunHausa.com cewa:

Advertising

“Jiya an tashi daga kallon ball, na fito kowa yana fitowa da misalin karfe sha daya saura kwata. Mun bar shi yana kwance, har da zan tashe shi, sai wani ya ce in bar shi tunda na ga mutane sai wucewa su ke yi babu wanda ya taba shi sai nima na wuce.

“Sai da safen nan na ji labarin wani ya rasu a silma. Sai na ce ba dai wannan mutumin da ya ke kwance a silima mai kaya masu ruwan kwai ba. Sai aka ce min ai ko a lokacin ya zama gawa.

“A gidan kallon kwallo na Queen Cinema lamarin ya faru. Ban san ko damuwar faduwar bangarensu ba ne ya kashe shi ko kuma lokaci ne ya yi ba.

“Ba a fitar da shi daga gidan kallon kwallon ba sai yau da safe saboda kowa ya watse ya bar shi a wurin.”

Muna rokon Allah yaji kansa yay masa Rahama Ameen summa Ameen.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button