Labarai

An kai kudin fansar wani yaro wajan ‘yan garkuwa da mutane amma yaki komawa wajan iyayan sa sabida yafi jin dadin zama a can

Wani karamin yaro kuma Dalibi a makarantar Bathel Baptist High School dake jihar Kaduna wanda ‘yar garkuwa da mutane suka sace shi, ya bayyana cewa yafi jin dadin zama a wajan masu garkuwa da mutane bayan da suke sake shi.

Masu garkuwa da mutanen dai sun sace wasu Daliban makarantar bathel Baptist High School guda dari da ashirin da daya (121), wanda har da karamin yaron a ciki.

A ranar 5 ga watan Yulin 2021 ne ‘yan ta’adda suka kai hari cikin makarantar dake kan titin Kaduna-Kachia, a wani kauyen mai suna Damishi da ke karamar Hukumar Chikun inda suka yi awon gaba da Daliban makarantar guda dari da ashirin da daya (121).

Shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa reshen jihar Kaduna mai suna “Rabaran Joseph John Hayab” shi ne ya bayyana hakan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kamr yadda Rabaran Joseph John Hayab ya fadi cewa, duk da an biya masu garkuwa da mutane kudin fansar yaron sabida ya kafe yace shi ba zai dawo gida wajen iyayen sa ba domin yafi jin dadin zama a wajan su.

Inda yaron yace, shi zai cigaba da zama a wajan masu garkuwa da mutanen wanda aka alajanta hakan da cewa, masu garkuwa da mutanen suna bashi abubuwan da yake so a duk lokacin da suka kai hari wani wajan suka samo kaya.

Sannan ance yaron ya sanar da masu garkuwa da mutanen cewa, shi baya son komawa gida wajen iyayan sa sabida ana dukan sa a duk lokacin da ya aikata wani laifi.

Lamarin ya jefa mutane cikin tashin hankali da rudani bayan haka kuma, masu garkuwa da mutanen sun rike wanda yake kai musu kudin fansa bayan da ya kai kudin fansar wannan yaron da yace baya son komawa wajan iyayan sa.

Inda suka yi kira da jami’an tsaro domin su taimaka su karbo wannan yaron daga hannun ‘yan a’addan masu garkuwa da mutane, da ma sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button