Advertising
Advertising
Labarai

Jami’an ‘yan sanda suna kama wani yaro bayan yayi garkuwa da kanwarsa yana neman kudin fan sa

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina da ke Arewa maso yammacin Najeriya sun kama wani yaro mai mai suna Abubakar Abdulbasir, da zargin satar wata karamar yarinya ‘yar gidan kawun sa mai shekaru hudu 4 a duniya.

Advertising

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar “SP Gambo Isah” shi ne ya gabatar da yaron mai suna Abubakar Abdulbasir mai shekaru goma sha takwas 18, wanda yake zaube a marabar kankara dake karamar hukumar malumfashi dake jihar katashina ga manema labarai a ranar Juma’a a hedikwatar su da ke Katsina.

Wani mutumi ne mai suna sanusi Abubakar ya kawo rahoto ga jami’an ‘yan sandan cewa , ‘yar sa ta bata tun ranar sha takwas 18 ga watan janairu, ‘yar tasa mai suna halimatu wanda take da shekaru hudu 4 da haihuwa sunyi duk kokarin da suke amma abin yaci tura.

Amma daga baya Abubakar wanda shi ne mahaifin yarinyar da ta bata ya sami kiran waya kan cewa, ya kawo naira dubu saba’in N70,000 ko a kashe ‘yar tasa, da jin haka ya kawo kara wajen ‘yan sanda.

Advertising

Su kuwa ‘yan sanda wanda sun kware wajan bincike masu garkuwa da mutane wato suka bazama wajen bincike, inda kuma sukayi sa’a suka kama wani yaro mai suna Abubakar Abdulbasir dan shekara goma sha takwas 18 da ke marabar kankara a karamar hukumar malumfashi.

Bayan kama yaron ya bayyana musu cewa, dalilin da yasa har ya sace wannan yarinyar wacce kanwace a wajan sa, domin ana binshi bashin naira dubu goma N10,000 na wata hula qube da ya saya yake son ya biya amma bai sami kudin ba.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin yaron a lokacin da ‘yan sanda suka kama shi suke masa tambayoyi.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button