Advertising
Advertising
Labarai

Masha Allah: Jarumin Fina Finan Kudancin Nigeria Jim Iyke Ya Karɓi Addinin Musulunci

Daga Aliyu A Tsiga

Advertising

Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood na Najeriya, Jim Iyke, ya bayyana cewa ya bar addinin Kiristanci kuma ya Musulunta. A cewarsa ya yanke shawarar ne bayan karanta littafai daya zurfafa da kuma fayyace abubuwa da dama.

Hakan na zuwa ne bayan da ya bayyana yadda ya haɗu da wata mata musulma a kwanan baya inda ya bayyana hakan saboda bambancin addini. Fitaccen jarumin a cikin faifan bidiyon ya yi kira da a kawar da ra’ayin addini, yana mai cewa mutane da dama na ci gaba da fuskantarsa ​​har yau.

Ya ƙara da cewa mutane na iya zama tare cikin lumana duk da bambancin ra’ayi na rayuwa, addini, siyasa da dai sauransu.

Advertising

Muna rokon Allah ya dauwamar dashi cikin wannan addini da babu kamar sa ya kuma kara karkato kan sauran kafurai da su gane gaskiya.

Mungode da bibayar shafin mu a ko da yaushe, Ku cigaba da Kasancewa damu dan samun zafafan labara.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button