Advertising
Advertising
Labarai

Kalli video Wani Dan Damfara da asirinsa ya tonu a cikin Coci ranar Alhamis.

Daga Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)

Advertising

Dubun wani matashi ta cika inda aka kama shi a wata Coci da safiyar jiya Alhamis ya yi shigar mata.

An bincika jikin dan Damfarar an samu wayoyi guda uku da wadansu abubuwa da dama.

Bayan haka an tabbatar da cewa matashin dan damfara ne (Yahoo boy) inda yake amfani da kafar sadarwa ta Facebook da sunan mace ya na damfarar mutane da sunan mace, zuwa yanzu wannan matashi yana hannun ‘yan sanda, duk da jami’an tsaron sun ce zuwa yanzu basu san me ya kawo shi Coci ba.

Advertising

Hukumar yan sanda tana cigaba da bincike akan wannan matashi, takuma ce da zarar sun gama bincike zasu mikashi hanun kotu domin ya girbi abinda ya shuka.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button