Labarai

Da tabarya nai amfani wajen Kashe kishiyata cewar wata mata.

Wata mata ta kashe kishiyata har lahira wajen Amfani tabarya a kauyen Gar dake jihar Bauchi.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda jihar Ahmed Wilil ne ya bayyana faruwar wannan lamari a wani zama da yaya da manema labari a jihar.

Ya ce mijin wanda ake zargin ne ya kai rahoton faruwar lamarin a hedikwatar ‘yan sanda ta Maina-Maji a ranar 22 ga Nuwamba, 2022.

“A ranar 22 ga watan Nuwamba, 2022 da misalin karfe 6:00 na yamma, wani Ibrahim Sambo magidanci mai shekara (40) da ke unguwar Gar kauye Pali, karamar hukumar Alkaleri, ya zo hedikwatar Yan sanda ta Maina-maji, inda ya kai rahoto. Haka kuma da misalin karfe 12:00 na safe matar sa ta biyu Maryam Ibrahim (20) mai adireshi daya sanye da fulawa ta shiga dakin matar sa ta farko mai suna Hafsat Ibrahim mai shekaru 32 mai adireshin guda daya ta buge ta da mari a kai.

Wadda aka halaka din ta samu raunuka da dama a jikinta, An mikata wani asibiti dake kusa dasu inda likitan ya tabbatar da rasuwar matar.

A halin yanzu matar data aikata laifin ta shiga hanun hukumar yan sanda inda sukace da zara sun gama bincike zasu mikata gaban alkali domin ta girbi abin da ta shuka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button