Fati muhammad tayi zazzafan martani da Allah ya isa ga mutumin da yayi mata kazafi
Fati muhammad tayi zazzafan martani da Allah ya isa ga mutumin da yayi mata kazafi
Duk da kasancewar jaruma Fati Muhd bata fiya kasancewa cikin masu shiga cece kuce a shafukannsada zumunta ko tankawa masu yi mata tsokaci na rashin gado ha, amma wannan karon wani ma’abocin Tiktok ya kure ta har yasa ta fito tayi masa Allah ya isa.
Biyo bayan cece kuce da akayi a kan batun ciko da ya gabata jarumar duk da a lokacin da ake tsaka da abin bata ce komai ba sai da kurar ta lafa ganin wasu har kawo yanzu basu daina zuwa shafin mata suna ce musu ciko phone sere ba yasa jarumar ta fito ta magantu gami da bada shawara ga masu wannan sara da su bari haka a bar abin ya wuce.
Sai dai koda wannan jawabi nata sai wani a sashen sokaci yayi mata wani irin zagi mara dadinji gami da kiran ta da mayya ragowar askarawa da sauran kalamai kazamai wanda hakan yasa jarumar ta fito
ta nuna rashin jin dadin ta gami da yi masa Allah ya isa.
Kana ta bayyana ita bata taba zaman kasar waje sai ingila shima zaman da tayi da auren ta tayi kuma auren yana mutuwa ta dawo gida da zai ce mata ragowar askarawa game da batun bilicin kuwa tace bata taba bilick kwaiiya ko ko shekararuta
nawa baza ta daina ba dan mace sai da kwalliya.
Da dama jarumai da fitattun mutane kan yi fama da wannan batu na cin zarafi a shafukan sada zumunta wato cyber bullying sanda laifi ne mai zaman kansa
da yake da sashi a kundin hukunta laifuffuka da dokoki amma a arewa ya zama kamar ba laifi ba idan mutum ya kasa hakuri ya dauki mataki kuma ace yayi rashin hakuri ba girman sa bane ya kamata
dai in an daki jakiKe dukan taiki Allah yasa mu dace.
Ga cikekkiyar bidiyon a kasa domin ku kalla.