Advertising
Advertising
Labarai

Datti Assalafiy yayi zafaffan raddi akan wakar Davido da Logosolori ta bataci ga addini

Datti Assalafiy yayi Zafaffan Raddi akan Wakar Davido da Logosolori ta ɓataci ga addini

Wasu matsáfan mawaka ‘yan kabilar Yarbawa Davido da Logosolori sun shirya waka a Masallaci suka wulakanta Sallah da Musulmai mukeyi a matsayin bauta wa Allah Ubangijinmu.

Advertising

Wannan cin zarafi ne da batanci mai girma ga addinin Musulunci da Musulmin duniya, sun tozarta Sallah matukar tozartawa.

Ya zama wajibi shugabannin Musulmin Nigeria su dauki matakin shari’ah akan wadannan matsafân mawaka ‘yan kungiyar cult!sm, domin wannan abinda sukayi umarni ne na kungiyarsu ta tsafi

Yana daga cikin dabi’ar mawaka da suka shiga kungiyar asiri don suyi suna a duniya, su kan fito su yi abu na wulakanta Musulunci irin wannan.

Advertising

Idan kuka zurfafa bincike akan Davido zaku tabbatar dan kung!yar asiri ne mai karfi a duniya wanda hatta ruh!n mutane yana sadaukarwa, yayi wannan abin ne da manufa wanda ya shafi kungiyarsu na as!ri, kuma sun bayyana tambarin kungiyarsu na cult!sm cikin bidiyon da sukayi suka wulakanta Sallah.

Ba wai kira ga Musulmai su dena bibiyarsu ba, matakin gaggawa ya kamata a dauka a kansu, duk da na san yana da karfi.

Yaa Allah Ka daukaka Musulunci da Musulmaiأمين.

Advertising
Back to top button