Labaran Kannywood

Bayan rasuwar Sani Garba SK Jarumin shirin Izzar so Lawan Ahmad ya bayyana wasu halayen marigayin

Marigayi Sani Garka Sk na daga cikin Jaruman fina-finan Hausa da ya jima ana mirginawa da shi, domin ya faro tun daga wasan dabe sannan ya tobe Television kadan da kuma inda ya dauki mafi rinjayen Iokaci wato Home video.

Bayan kwarewa da iyawa Sani yana daga cikin Jarumai masu tarbiyyya wato Discipline wajan gudanar da sana’arsa ta film, misali, yana kiyaye lokacin zuwa aiki in an gayyace shi sannan bai cika korafin a yi maza a sallame shi a location ba kamar yadda wasu.

Jarumai kan yi musamman in sun ga sun sami daukaka kazalika da wahala ya sami sabani da Daraktansa ko sauran Jarumai ‘yan uwan sa a location, Sani ya sami kyakkyawar shaidar iya mu’amala da abokan Sana’a kwarai da gaske.

Ni a karan kaina babu abin da zan ce da rayuwar Sani SK sai San barka domin sun taso a wannan masana’anta tare da su Alasan Kwalle kuma suna daukata a matsayin yayansu a rayuwa.

Zan iya tunawa wata shekara mun kai ziyara Junhuriyar Niger domin gabatar da wasa a babban dakin taro na kasar wato Pale de congre, inda aka sami sabani wajan biyanmu hakkinmu.

Don haka ba wai su Ali Nuhu da Halisa da Biba da sauran matasan wancan lokacin ba, a, a hatta Ni kaina duka mun rikice muna neman rigima da wadanda suka gayyace mu, amma Sani SK kadai Allah ya sanyawa nutsuwa inda ya dinga kai mari yana kai gwauro sai da ya ga ya dinke barakar.

Ta fuskar Sana’a kuwa SK kwararre ne kamar yadda
kowa ya shaida ya iya action film musamman a Na tabbata kyakkyawan halin Sani ne, ya sanya abokan Sana’a suka dinga dawainiyar kula da lafiyarsa a lokacin da ya shiga rashin laflya.

Tsohon Malamin makarantar Islamiyya Kuma Sha’iri wanda ya yi fice wajan kasidar yabon Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. Allah ya jikansa ya gafarta masa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button