Sojoji sun sami nasarar hallaka ‘yan ta’adda da dama tare da konewa maboyar shahararran dan ta’adda Bello Turji
Sojoji sun sami nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama tare da konewa maboyar shahararran dan ta'adda Bello Turji
Rahotanni sun bayyana cewa, an illata shahararran dan ta’addan nan Bello Turji wanda shine jagoran ‘yan ta’adda a yanzu, inda ya sami raunuka sosai a yayin da jirahen Sojoji suka kai har maboyar su da kuma inda ‘yan fashin Dajin suke.
Kamar yadda Jaridar PRNigeria ta jiyo daga wata majiya a bangaren Jami’an tsaro, haka zalika gamayyar rundunar dakaru ta sintirin hadin kai sun hallaka ‘Yan fashin Dajin Zamfara da Sokoto a safiyar ranar Lahdi.
Majiyar sirri ta rundunar soji ta tabbatarwa PRNigeria cewa: An kai gagarumin harin da a ka kai a dajikan ta sama da kasa ne a Shinkafi da ke Zamfara, Bafarawa, Isa da kuma Sabon Birni a Sakkwato.
Kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito majiyar ta bayyana cewa: Kawo yanzu dai ba a tantance adadin yan ta’addan da a ka hallaka a hare-haren ba.
PRNigeria ta jiyo cewa: Sauran yan fashin dajin da su ka samu raunuka kuma su ka tsere, sun gamu da ajalinsu a hannun sojojin ƙasa a cikin jeji.
Majiyoyin tsaro na sojoji sun tabbatar da cewa hare-haren da a ke kaiwa ƴan ta’addan a Arewa-Maso-Yammacin Nijeriya na haifar da ɗa mai idanu kuma a na samun nasara.