Advertising
Advertising
Labarai

An tsinci gawar wata jarumar Fim mai suna Takor Veronica a bakin Otel a Benue bayan an kashe ta

An tsinci gawar wata jarumar Fim mai suna Takor Veronica a bakin Otel a Benue bayan an kashe ta

A wani labari da muka samu daga shafin Hausaloaded kan cewa, an tsinci gawar wata jarumar Nollywood dake kudancin Nageriya mai suna Takor Veronica a cikin wani Otel a jihar Benue.

Advertising

An gano gawar jarumar ne kimanin sati daya bayan da tayi bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ta, wanda a turance ake kira da Happy Birthday.

A cewar shafin Legit ta ruwaito cewa, an tsinci gawar jaruma Takor Veronica a cikin wani Otel a unguwar Nyinma na Makurdi.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Benue “SP Catherine Anene” ta tabbatar da afkuwar lamarin, a cewar kakakin ‘yan sandan an kama wasu mutane uku 3 wanda ake zargin da sa hannun su a mutuwar jarumanr.

Advertising

Kamar yadda yace: An kawo rahoton mutuwar wata mata a otel amma muna jiran bayani daga likitoci. Ba mu ga alamun rauni a jikinta ba. Don haka gwajin likitoci zai sanar da mu sanadin mutuwarta. Matar da ta mutu tana sanye da tufafi; ba mu ga alamar rauni a jikinta ba.

An kama mutane uku da ake zargi da hannu a wannan, za su bamu karin bayani. Ba za mu iya cewa kashe ta aka yi ba domin ba mu ga alamar rauni ba, in ji ta.

Inda abokanta da kuma abokan aikin ta suka yi ta sakon ta’aziyya a shafin sada zumunta.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button