Labarai

Har yanzu dai Sheikh Isah Ali Fantami yana shan maganganu a wajan Mutane sabida yaki magana kan ta’asar da ake a Nageriya

Sanin kowa ne yadda ake ta zungurin Malamin addinin kuma minista Sheikh Isah Ali Fantami a kafafan sada zumunta tun bayan da hare-haren masu garkuwa ya tsanan ta ba tare da Malamin ya fito yayi kira ko korafi ga Gwamnati a karatuttukan sa kamar yadda ya saba ba.

Wanda ada an san Malamin da rashin tsoro wajan kalubalantar Gwamnati kafin ya haye kan kujerar Minista.

An dinga wallafa maganganun Malamin tare da korafe-korafen koken da yayi sabida bakin cikin irin yadda ake zaluntar talaka, to amma mai yasa a wannan lokacin da yake kan kujerar Minista ba zai fito yayi irin wannan kukan ba duk da ta’asar da ake ko dai yana kare kujerar sa ta Minista ne.

A cikin bidiyn dake kasa wanda Tashar “Tsakar gida” dake kan manhajar Youtube ta wallafa, zaku ji cikekken labri akan yadda mutane suke ta maganganu akan Sheikh Isah Ali Fantami yaki fitowa yayi magana game da ta’asar da ake a Nageriya Musammam Arewacin Kasar.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button