Advertising
Advertising
Labarai

Sai da na cire Hijabi sanna na sami daukaka a Duniya har naci gasar Sarauniyar kyau, cewar Shatu Garku

Sai da na cire Hijabi sanna na sami daukaka a Duniya har naci gasar Sarauniyar kyau, cewar Shatu Garku

Matashiyar nan wacce ta lashe gasar sarauniyar kyau ta Najeriya wato Shatu Garko, ta bayyana kalubalen da ta fuskanta a matsayin ta na mace mai sanya hijabi.

Advertising

Shatu Garko wacce take da shekaru goma sha takwas 18 wacce ta lashe gasar ta karo na arba’in da hudu 44 ta zama mace ta farko mai sanye da hijabi da ta lashe gasar, inda ta buge sauran mutum goma sha takwas 18, ta bayyana hakan ne a yayin wata zantawa da tayi da jaridar PUNCH da labarunhausa.

Kamar yadda shatu Shatu Garko ta bayyana cewa, da farko ta sha kalubale sosai sabida hijabin da take sanyawa wanda a cewar ta kamfanoni da dama sun ki yin aiki da ita sabida ta na sanya hijabi.

Inda suke shawartar ta da cewa sai ta cire hijabi idan har tana son ta samu nasara a sana’ar tallan kayan kawa.

Advertising

Shatu Garku ta kara da cewa, nan kai shekara daya ba da zama mai tallan kayan kawa, bayan na kammala makaranta na zauna a gida sabida annobar cutar korona, sannan na tsani zama hakanan bana yin komai sai na yanke shawarar na gwada sa’a ta a harkar tallar kayan kawa.

Ta kara da cewa, na sha wahala a gwajin farko da nayi da farko sun dauke ni amma daga baya suka fadamin cewa, ina bukatar samun gudanarwa mai kyau inda suka ki yin aiki da ni sai dai hakan bai sanya guiwoyina sarewa ba amma ya kara min karin karfin guiwar domin na kara dagewa sosai.

Shatu Garku tace, Mahaifiyata ta bayyana min cewa, ba daga farawa kawai zaki samu nasara ba inda ta sanya ni na fahimci cewa dole sai mutum ya fadi kafin ya sami nasara.

A farkon fara wannan sana’ar tawa na sha wahala sabida hijabin da nake sakawa Kamfanoni da dama sun ki bani damar aiki da su, kuma a lokuta da dama an sha fada min cewa sai na cire hijabi na idan ina son nayi nasara a matsayin mai tallar kayan kawa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button